’Yan sanda sun kama wani dan bindiga, wanda suka kwato shanun sata 55 a hannunsa a Karamar Hukumar Karaye ta Jihar Kano.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, Usaini Muhammad Gumel ya bayyana cewa, dan ta’addan ya tabbatar musu cewa dubunsa ta cika ne a yayin da yake kokarin dawowa Jihar Kano da zama.
- Kotu ta yi wa matar aure ɗaurin rai-da-rai saboda kashe dan kishiyarta a Kano
- Gobara ta halaka wani yaro dan shekara 4 a Kano
Dan bindigar, wanda ba a bayyana sunansa ba ya ce, ya gudo ne daga sansanin ’yan bindiga na Maidaro ne da ke Malumfashi a Jihar Katsina, ya biyo ta Birnin Gwari a Jihar Kaduna ya shigo Kano.
Ya kuma bayyana cewa, ya gudo daga Malumfashi ne sakamakon rikici da ke tsakaninsa da gungun jagoran ’yan bindiga Boderi Isiya.
A cewar dan ta’addan, an kashe jagoran bangarensu da mataimakinsa a fadan, shi ne ya gudo da shanu 55 da tumaki shida da bindigogi uku kirar AK-47, zai koma dajin kananan hukumomin Karaye da Gwarzo na Jihar Kano da zama.
Kwamishinan ’yan sandan ya shaida wa ’yan jarida cewa, wanda ake zargin ya tabbatar wa ’yan sanda masu bincike cewa, an sha zuwa da shi yin garkuwa da mutane a jihohin Katsina da Zamfara da kuma Kaduna.
Ya ci gaba da cewa, ana farautar sauran ’yan bindigar da suka tsere domin su fuskanci hukunci.