✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ɗan bindiga, an kwato kuɗin fansa a Kaduna

Rundunar ta ce an miƙa wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wani ɗan bindiga tare da ƙwato kuɗin fansa a hannunsa.

Kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan ne, ya tabbatar da kamun a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kaduna.

Hassan ya ce, “A ranar 22 ga Mayu, da misalin ƙarfe 10:00 na safe, ’yan sanda a yankin Saminaka sun kama wani da ake zargin ɗan bindiga ne mai shekara 33, dan asalin Tudun Wada Mariri a yankin Upara Warsapiti da ke ƙaramar hukumar Lere a jihar.

“An same shi da wata jaka ɗauke da kuɗi Naira 347,000, adduna, da wasu layu,” in ji Hassan.

A yayin masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin satar mutane domin karabar kuɗin fansa tare da wasu mutane uku a daga ƙauyen Binchim da ke ƙaramar hukumar Bassa a Jihar Filato.

Ya ce kuɗaɗen da aka ƙwato wani kaso ne na kuɗin fansa da ya karɓo daga sace wasu mutane biyu a ranar 17 ga watan Mayu, 2024 a lokacin da suke aiki a wata gona.

“Sun kai waɗanda suka sace zuwa tsaunin Binchim, sannan sun sake su a ranar 20 ga watan Mayu, 2024.

“Ana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran masu hannu a sace mutane tare da shi,” in ji Hassan.

Ya ƙara da cewa an miƙa wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) na jihar don ci gaba da bincike.

Hassan ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Dabigi, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro a faɗin jihar.

Ya kuma yaba da yadda jama’a ke ci kara ba su haɗin kai, sannan ya bukaci su zama masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu ga jami’an tsaro.