Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya tsallake rijiya da baya sanadiyyar wani hari da aka kai wa ayarin motocinsa a kan hanyarsa ta halartar wani uzuri a Abuja.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo ne ya bayyana hakan a Yammacin wannan Lahadin.
- ’Yan ta’adda sun kashe jami’in kwastam a Yobe
- Ana tsananin buƙatar man fetur saboda ayyukan asibitoci a Gaza — MDD
Ya ce harin da aka kai wa gwamnan ya auku daura da Babbar Sakatariyar Kwali da ke Abuja da misalin karfe 4:00 na Yammacin wannan Lahadin bayan ya taso daga Lokoja.
A cewar Fanwo, maharan wadanda suka yi shiga ta kakin soja sun yi wa ayarin motocin kwanton bauna, inda suka rika yi musu ruwan harsasai na bindiga.
Sai dai Kwamishinan ya ce harin wanda jami’an tsaro suka tari hanzarinsa cikin gaggawa, ya faru ne a sakamakon yadda wasu ke ƙoƙarin tayar da tarzoma gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a watan gobe.
Ya ce Gwamnatin Kogi na kara tabbatar da tsaron al’umma jihar da ba za ta bari wadanda miyagun ’yan siyasa masu neman tayar da zaune tsaye su yi nasara ba.
“Muna kira ga al’ummar jihar da su kasance masu lura da ankarar da mahukunta a kan duk wani motsi da ba su aminta da shi ba.
“Nauyin gwamnati ta tabbatar da tsaron al’ummarta da dukiyarsu, saboda haka ba za mu bari a yanzu siyasa ta sarayar da amincin da aka ci moriyarsa a jihar na tsawon shekara takwas ba.”