Kotun hukunta masu karya dokar kariyar COVID-19 a Jihar 25 ta tura mutum 25 da ta kama da laifi gidan yari.
Akalla mutum 200 ne jami’an tsaro suka tsare saboda karya dokar COVID-19 da Gwamnatin Kano ta shimfida wanda daga cikin mutanen aka ci wasu tara.
- Matakin Gwamnatin Kano kan Sheikh Abdujabbar ya yi daidai —JNI
- Yerima ya zama sabon kakakin Rundunar Soji Kasa ta Najeriya
- El-Rufai ga Gumi: Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba
- An kama kani a cikin masu garkuwa da matar wansa a Zariya
“Mun gode Allah mutanen Kano na bin dokar sanya takunkumi don kare lafiyarsu.
“Duk masu kunnen kashi da suke kin saka takunkumi za su fuskanci hukunci. Don haka dokar kariyar COVID-19 ta zauna ke nan,” a cewar Shugabna Hukumar Kula da Hanya ta Jihar Kano (KAROTA) Baffa Babba DanAgundi.
Bayan fara aiki da dokar sanya takunkumi, Gwamnatin Kano ta kafa kotun tafi-da-gidanka akalla 21, wanda DanAgundi ke jagoranta.
Ya bayyan cewa an kama masu karya dokar har mutum 102 da aka ci tarar N5,000 kowanensu.
Ya sake jan hankalin shugabanin kasuwanni da tabbatar da bin dokar kariyar.
Da yake jawabi, Kwamishinan Yada Labaran jihar, Muhammad Garba ya ce sabuwar dokar za ta tabbatar da kare mutane daga kamuwa da cutar COVID-19.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakin ne saboda yadda cutar ke kara yaduwa a jihar tun bayan sake bullarta a karo na biyu.
Ya ce duk wanda kotun tafi-da-gidanka ta samu ya karya dokar to za a hukunta shi yadda doka ta tanada don haka ya ja hankalin jama’ar jihar da su kasance masu bin doka a kodayaushe.