An jiyo karar harbe-harbe a ranar Lahadi a gidan gyaran hali da ke Jos, babban birnin Jihar Filato.
Wakilinmu ya gano cewa an fara jin harbe-harben ne wajen misalin karfe 5:30 na yamma.
- Tikitin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya kai N7,000 a hannun ’yan ka-yi-na-yi
- Mun bankado sunan jariran da ake biya albashi daga lalitar Borno – Zulum
Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a ilahirin yankin da gidan gyaran halin yake.
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS), Jeff Longdiem, ya yi alkawarin cewa zai kira shi daga baya.