✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai hare-haren ta’addanci fiye da 5,000 cikin shekaru 3 a Yammacin Afrika

A cikin watanni 3 na bana an samu hare-hare sama da 840.

A cikin shekaru 3 da suka gabata, Yammacin Afirka ya fuskanci sama da hare-haren ta’addanci 5,300 abinda ya yi sanadiyar hallaka mutane kusan 16,000, yayin da a cikin watanni 3 na wannan shekarar aka samu hare-hare sama da 840.

Ministan tsaron Ghana Dominic Nitiwul ne ya bayyana hakan a yayin da manyan hafsoshin tsaron kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS suka fara taron kwanaki 2 a kasar Ghana domin nazari a kan matsalolin tsaron da suka addabi yankin da kuma yadda za su hada kai domin tunkarar su.

A cewar Dominic Nituwul, matsalar tsaro daga kungiyoyin da ke dauke da makamai da masu aikata manyan laifuffuka na karuwa a yankin.

Nitiwul ya bukaci musayar labaran sirri a tsakanin jami’an tsaron domin tunkarar ayyukan wadannan bata-gari wadanda ke jefa rayuwar jama’a cikin hadari.

Ministan ya ce a matsayinsu na kwararu ya dace su yi watsi da batun maganar al’ada da addini da kasa wajen hada kai a tsakanin su da zummar samun nasara.

Najeriya da Nijar da Mali da Burkina Faso na daga cikin kasashe 15 da ke cikin kungiyar da ke fama da matsalar tsaron dake da nasaba da ayyukan ta’addanci, yayin da kasashen Ghana da Jamhuriyar Benin da Cote d’Ivoire ke fargabar fantsamar tashin hankalin zuwa kasashensu.