✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kafa kwamitin bincike na musamman kan harin NDA

Za a gudanar da binciken kan yadda aka kai harin NDA.

Manyan Shugabannin Rundunar Sojin Najeriya a ranar Laraba sun kafa kwamiti na musamman don bincikar yadda aka yi ‘yan bindiga suka kai hari makarantar horar da sojoji ta NDA da ke Jihar Kaduna.

Aminiya ta ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar ranar Talata suka kai hari cikin NDA, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar dakarun soji biyu, sannan suka sace soja daya.

Rundunar sojin ta bakin jami’inta na hulda da al’umma, Manjo-Janar Benjamin Sawyerr, ta ce an kafa kwamitin ne don hana faruwar hakan a gaba.

“Zan yi amfani da wannan dama wajen sanar da cewar NDA karkashin jagorancin Babban Hafsan Soji, ta kafa kwamiti na musamman don bincike yadda aka yi aka haihu a ragaya.

“Ina mai tabbatar muku da cewar za mu ci gaba da sanar da jama’a yadda ake ciki sannan ana ci gaba da bincike don ceto sojan da aka sace.

“Dakarun sojin Najeriya za su ci gaba da bincike don gano wanda suke da hannu a harin tare da gurfanar da su gaban shari’a,” cewar sanarwar.

Kazalika, rundunar sojin ta yi watsi da rahoton da ake yaduwa cewar dakarun da ke kula da na’urar CCTV sun yi bacci lokacin da lamarin ya faru.