karon farko an kaddamar da shafin kallon fina-finan Hausa da abubuwan da suka shafi al’adu da al’ummar Hausawa a Intanet, inda aka kaddamar da shafin mai suna Kallo.ng a Jihar Legas a ranar Litinin da ta gabata.
Babbar Manajar shafin na Kallo.ng, Maijidda Modibbo, ta shaida wa Aminiya cewa, shafin zai bunkasa al’adun Hausawa tare da bai wa dimbin al’ummar da za su rika ziyartar shafin nishadi.
- Kotun Myanmar ta daure Aung San Suu Kyi shekara 4 a kurkuku
- An tsinci gawar yara 8 a cikin tsohuwar mota a Legas
“A baya babu irin wannan shafi namu na Hausawa zalla, sai dai wadansu ba Hausawa ba ne kan bude, ganin zai fi dacewa mu yada al’adunmu da kanmu, kada mu yi sake wadansu su ba da labarinmu, abin da ya fi dacewa shi ne mu ba da labarinmu da kanmu,” inji ta.
Maijidda Modibbo ’yar asalin Jihar Kano ce da ta karanci aikin yada labarai a matakin digiri na biyu ta kuma shafe shekara 16 tana aiki a masana’artar yada labarai ta ce, shafin na Kallo.ng shafi ne da zai zo da ingantattu da salo na zamani domin jin dadin masu bibiyar shafin a daukacin kasashen Afirka da duniya baki daya, inda ta ce wake da rayeraye hanyoyi ne na yada al’adu da kuma nishadantarwa.