✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An je kotu nema wa Buhari da gwamnoni wa’adi na uku

Ana neman kotu ta soke sashen da ya takaita su ga yin mulki sau biyu.

Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki ya maka Majalisar Tarayya da Ministan Shari’ia a kotu, yana neman kotun ta ba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni damar yin  wa’adi na uku a kan mulki.

Honorabul Charle Oko Enya, ya bukaci Babbar Kotun Tarayya da ke Abakaliki, Jihar Ebonyi, ta soke sashen kundin tsarin mulki da ya kayyade wa gwamnoni da shugaban kasa wa’adi biyu na yin mulki amma ya bar ’yan majalisa su yi har sai abin da hali ya yi.

Charles ya ce tanadin na kudin tsarin mulki zalunci ne da take hakkin dan Adam, musamman mutane irin Shugaba Buhari da gwamnoni.

Takardar karar da lauyansa, Barista Agboti Iheanacho, ya gabatar a ranar Laraba, ta ce “Sashe na 137(1)(b) an Kundin Tsarin Mulkin Najeiyra na 1999 (da aka yi wa gyara) da ya takaita Shugaban Kasa yin mulki na wa’adi biyu kacal, kowannne shekara hudu, ba shi da muhalli saboda ya nuna wariya tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki a gwamnatin Najera, saboda haka ya haramta kuma ba zai yi aiki ba.”

Charles Enya, wanda shi ne Sakataren Yakin Neman Zaben Buhari a 2019 ya yana “neman Kotun ta umarci Majalisar Tarayya da Akawun Majalisar su soke su kuma cire sashen na 137(1)(b) da kuma Sashe na 182(1)(b) daga kundin tsarin mulkin.”

Yana kuma neman Kotun ta umarci Ministan Shari’a, ya ba wa Gwamnatin Tarayya duk goyon bayan da ya kamata domin Majalisar Tarayya da Akawun Majalisar su fara aikin cire sassan kudin tsarin mulkin da ya ce sun nuna wariya kan yawan wa’adin mulki tsakanin ’yan majalisa da bangaren zartarwa.

Charles Enya, wanda ake sa ran fara sauraron kararsa a cikin mako biyu, ya kara da cewa tsarin da ake amfani da shi a Najeriya, ya ci karo da Yarjejeniyar Kasashen Afirka na kare hakkokin da kuma ’yancin mutene.

Wadanda yake karar su ne Akawun Majalisar Tarayya, Mohamed Sani-Omolori, Majalisar Tarayya da kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami.