Ma’aikatar Kula da Harkokin Mata ta Jihar Yobe tare da haɗin gwiwar Hukumar Samar da Ayyukan Yi ta Ƙasa (NDE) sun ƙaddamar da shirin horar da mata 300 sana’o’i daban-daban.
Da ta ke bayani a yayin buɗe taron, Kwamishiniyar ma’aikatar mata ta jihar, Ya-Jalo Badama, ta jaddada muhimmancin koyon sana’o’i don bunƙasa cigaban tattalin arziƙi da dogaro da kai a tsakanin mata.
Kwamishiniyar ta buƙaci mahalarta taron da su yi amfani da damar da aka ba su yadda ya kamata domin an zaɓo su ne bisa cancanta.
Tun da farko a jawabinsa na maraba, Kodinetan Hukumar Samar da Ayyukan Yi ta Ƙasa, wanda Mallam Habu Dauda Chiroma ya wakilta, ya ce horon zai ta’allaƙa ne kan ayyukan samun kuɗin shiga, da hanyoyin samar da aikin yi a intanet.
Ya jera tsare-tsaren da suka haɗa da harkokin kasuwancin kai da kai ga mata 100 marasa aikin yi, da ayyukan samar da kuɗaɗen shiga ga mata 100.
Sauran sun haɗa da mata 50 da ba su da aikin yi da za su shiga sana’ar koyar da sana’o’in hannu yayin da wasu mata 50 kuma za a horas da su kanharkokin kasuwanci ta intanet.
A nasa tsokacin, shugaban sashen kula da ƙananan sana’o’i na hukumar NDE a Jihar Yobe, ya bayyana irin nasarorin da aka samu a irin waɗannan shirye-shirye a faɗin Najeriya.
Ya kuma jaddada muhimmancin shirin wajen ƙarfafa wa matan jihar don su tsaya da ƙafafunsu.
Yayin da ta ke miƙa godiyarta ga NDE a madadin ma’aikatar, sakatariyar ma’aikatar harkokin mata, Hajiya Zainab Ago Muhammad, ta buƙaci waɗanda suka amfana da su mayar da hankali tare da sadaukar da kansu wajen koyon sana’o’i.
Ita ma babbar jami’ar kula da harkokin mata ta Majalisar Dinkin Duniya da ke jihar, Hajiya Fatima Paga, ta shawarci waɗanda suka ci gajiyar shirin yadda ya kamata.
Wasu daga cikin mahalarta taron da suka yi jawabi sun bayyana jin daɗinsu tare da nuna sha’awar koyon sabbin fasahohin da za su ba su damar ƙirƙiro sana’o’i da kuma bayar da gudunmawa ga al’ummarsu.