Hukomin tsaro sun tabbatar da kashe wasu ‘yan bindiga hudu yayin wani artabu a Kananan Hukumomin Chikun da Birnin Gwari na Jihar Kaduna.
An samo manyan bindigogi uku da wani gatari daya a hannun ‘yan bindigar da ake kyautata zaton sune masu addabar al’umma a yankuna daban-daban na Jihar.
- Sojoji sun fatattaki ’yan Boko Haram daga hanyar Damaturu zuwa Maiduguri
- Abin da ya kamata ku sani kan wasan Manchester City da Manchester United
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya inganta rahoton cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ya ce an samu wannan nasara ne biyo bayan rahoton da rundunar ‘Operation Thunder Strike’ ta samu ta hanyar tattara bayanan sirri a kan shige da ficen ‘yan bindigar a tsakanin kauyen Katika zuwa Antenna da ke Karamar Hukumar ta Chikun.
Aruwan ya ce dakaru sun yi wa ‘yan bindigar kwanton bauna a kauyen Antenne inda suka bude musu wuta da har aka samu nasarar kawar da hudu nan take.
Ya kara da cewa, an samu nasarar kashe karin wasu ‘yan bindigar yayin ruwan wuta ta sama da aka kai wa maboyarsu a Kananan Hukumomin Chikun da Birnin Gwari.
Kazalika, ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya yaba wa azamar dakarun dangane da jarumtar da suka nuna wajen samun galaba a kan ‘yan bindigar.