✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbe wani tsohon babban sojan sama da jikansa a Kaduna

Matar mamacin ta ce ’yan bindigar ba su dauki komai ba bayan kisan mutanen.

Wasu ’yan bindiga sun harbe wani tsohon babban sojan sama, Eya Bayis Mashal Mohammed Maisaka da jikansa a rigasa da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Aminiya ta gano cewa jikan nasa mai kimanin shekara 27, wanda sojan sama ne yanzu haka, yana aiki da kakan nasa ne a matsayin dogarinsa.

’Yan bindigar dai sun yi wa gidan marigayin da ke kan Titin Makarfi Road a Kaduna kawanya da misalin karfe 8:30 na dare sannan suka bude wuta.

Marigayi Mohammed Maisaka
Marigayi Mohammed Maisaka

Da take tabbatar da harin ga wakilin Aminiya, matar mamacin, Hajiya Fatima Maisaka, ta ce ’yan bindigar ba su dauki komai ba bayan kisan mutanen.

“Kawai sun shigo falonmu ne sannan suka harbe su ba tare da daukar komai ba. Hatta wayoyinmu ba su dauka ba,” inji ta.

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan, ya iske tarin masu jaje a gidan mamacin.

Kafin rasuwarsa, marigayi Maisaka shi ne shugaban asibitin MSK da ke Makarfi Road a Kaduna, kuma ya rasu ya bar matarsa da ’ya’ya da kuma mahaifiyarsa.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai amsa kiran wayar wakilinmu ba don jin ta bakin rundunar kan harin.