‘Yan bindiga sun harbe wani tsohon manemin takarar gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Sagiru Hamidu.
Rahotanni sun ce Alhaji Sagiru na daga cikin matafiyan da ‘yan bindiga suka tare a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadi.
- Najeriya A Yau: Yadda uba ya yi wa ’yarsa fyade har ta samu ciki a Bauchi
- Ya sakale maciji a jikin kofar gidan ’yan haya
Aminiya ta ruwaito cewa maharan sun harbe Alhaji Hamidu yayin da suka bude wuta kan matafiyan da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Lahadi daura da kauyen Rijana da ke kan babbar hanyar.
Wani da ya tsallake rijiya da baya da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun ribaci lalacewar da hanyar ta yi wanda hakan ya tilasta wa motoci tafiya sannu-sannu kuma a kan hannu daya.
Wakilinmu ya ambato wani matafiyi da ya kubuta yana cewa, ‘yan bindigar sun tare hanyar ne a kusa da kauyen Rijana tun da misalin karfe uku na rana inda suka shafe fiye da sa’a daya suna tafka ta’asa ba tare da sun fuskanci wata tirjiya ba.
“Sai da muka ja da baya sosai muka bayar da tazara mai nisan gaske bayan da muka ji harbe-harben ‘yan bindigar.
“Bayan akalla sa’o’i biyu sai muka hangi wasu motocin na biyo daya hannun, daga nan ne muka ci gaba da tafiya,” a cewar matafiyin.
Ya kara da cewa, “watakila maharan sun dauke matafiya da dama ko kuma sun tsere cikin daji saboda akwai motocin matafiya kimanin 15 da muka tarar yashe a hanyar yayin da muke ratsa ta wurin da harin ya auku.”
Kawo yanzu dai rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ba ta ce uffan a kan lamarin ba.