✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbe mutum 2, an sace ma’aikatan lantarki ’yan China 3 a Neja

An sace su ne a wurin aikin samar da lantarki da ke Zungeru a Jihar.

Akalla mutum biyu ne ’yan bindiga suka harbe har lahira, sannan suka sace wasu ma’aikata ’yan kasar China kuma su uku da ke aikin samar da wutar lantarki a madatsar ruwa ta Zungeru a Karamar Hukumar Wushihi ta Jihar Neja.

Aminiya ta rawaito cewa maharan, masu dimbin yawa sun kai wa ma’aikatan kamfanin Sino-Hydro da ke aikin wutar a wani tirken lantarkin da ke kauyen Gusasse da yammacin Talata.

Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane ya tabbatar da sace mutanen, amma ya ce ba zai iya tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba.

Shi ma da yake tabbatar da harin, kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce an harbe wani dan kasar Chinan ne da dan Najeriya, sannan aka sace wasu ’yan Chinan uku bayan musayar wuta da ’yan bindigar.

Ya ce, “Da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar hudu ga watan Janairun 2022, wasu ’yan bindiga dauke da makamai sun kai wa ma’aikata hari a tashar samar da wutar lantarki ta Sino-Hydro.

“Ma’aikatan sun hada da ’yan Najeriya da wasu ’yan kasar China da ke aiki a wajen wani tirken lantarki da ke kauyen Gusassa.

“To sai dai ’yan sanda na musamman da ke kula da wajen sun yi musayar wuta, sannan suka kubutar da hudu daga cikinsu, wasu kuma suka samu rauni, yanzu haka suna asibiti suna samun kulawa.”

Kakakin ya kuma ce a kokarin guduwa yayin musayar wutar, an yi awon gaba da ’yan China su uku.

Ya kuma ce tuni jami’an ’yan sanda da sojoji sun kaddamar farautar maharan da kuma kubutar da mutanen da aka sace.