✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An haramta amfani da Adaidaita Sahu daga karfe 10 na dare a Kano

Dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis.

Gwamnatin Jihar Kano ta haramta zirga-zirgar babur mai kafa uku wanda aka fi sani da Adaidaita Sahu daga karfe 10:00 na dare zuwa wayewar gari.

Wannan na kunshe a cikin sanawara da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba ya fitar a Litinin din nan.

A cewarsa, dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli, 2022.

Wannan na zuwa ne yayin da a baya-bayan nan aka rika samun rahotanni cewa, galibi ana amfani da Adaidaita Sahu wajen kai hare-hare tare da kwacewa jama’a dukiyoyinsu musamman wayoyin hannu.

A cewar Kwamishinan, gwamnati ta dauki matakin ne a karshen taron tattaunawa kan sha’anin tsaron jihar da ta gudanar da dukkan masu ruwa da tsaki.

Kwamishinan ya kara da cewa daukar matakin ya zama dole don tabbatar da tsaro wajen tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Kazalika, Kwamishinan ya yi kira ga direbobin baburan masu kafa uku da su yi wa wannan sabuwar doka da’a, domin kuwa duk wanda aka samu ya ketare zai dandana kudarsa.