Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta ce ta kashe mutum biyar da take zargin masu garkuwa da mutane ne domin neman kudin fansa a karamar hukumar Safana ta jihar.
Kakakin rundunar, SP Gambo Isa ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa ‘yan jarida a Katsina ranar Laraba.
Ya ce an kashe mutanen ne a ranar 27 ga watanOktoban 2020 da misalin karfe 4:00 na yamma a kauyen Tsakiya na karamar hukumar.
Kakakin ya ce, “Daga bayanan da muka samu da hadin gwiwar sojoji, rundunarmu ta sami nasarar kubuta daga hare-haren ‘yan bindiga a garin Tsakiya na Safana.
“’Yan bindiga da yawansu ya kai kimanin 200 dauke da muggan makamai ciki har da jigida da bindiga kirar AK47 sun kai hari tare da harbi kan mai uwa da wabi a kauyen.
“Hadakar jami’an tsaro sun yi musayar wuta da bata-garin inda a sakamakon hakan suka hallaka biyar daga cikinsu, da dama kuma suka tsere da raunuka a jikinsu,” inji shi.
Gambo ya kuma ce ‘yan bindigar sun kuma kashe wani mai tabin hankali mai suna Rabe Bala mai kimanin shekaru 30 bayan da suka hange shi a kauyen.
Kakakin ya kuma ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu mata su uku zuwa cikin daji lokacin da suke kokarin tserewar.
Ya ce yanzu haka dakarunsu sun dukufa wajen farautar mutanen da nufin kubutar da gawawwakin da suka kashe da kuma kama wadanda aka jikkata a cikinsu.