✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An halaka kananan yara da iskar gas a Syria

Akalla mutum 58 ciki har da kananan yara 11 ne suka mutu a wani harin da aka kai na iskar gas a kasar Syria. Hukumar…

Akalla mutum 58 ciki har da kananan yara 11 ne suka mutu a wani harin da aka kai na iskar gas a kasar Syria.

Hukumar Kula da Hakkin dan Adam na Syria ta ce wannan harin wanda aka kai yankin Sheikhoun da ke Idlib, ya sanya mutane da yawa sun suma, wasu kuma suka rika fitar da kunfa a bakinsu, sannan suka bayar da misalai da ilimin kimiyyar magunguna, inda suka tabbatar da cewa lallai an yi amfani da gas a harin.  

Cibiyar Edlib Media mai fafatukar yaki da danniya, sun watsa hutuna a kafofin sadarwa da suka nuna mutane ana ba su agajin gaggawa, ciki kuma har da matattun kananan yara.  

Idan ba a manta ba, an taba kai irin wannan harin garin Ghoutar kusa da baban birnin kasar a shekarar 2013, wanda ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane wanda har gwamnatocin turai suka zargi gwamnatin Syria da alhakin kai wannan harin, a yayin da ita kuma gwamnatin kasar ta zargi ‘yan ta’addan kasar.

Su kuma mutanen gari cewa suka yi an kawo harin ne da safiyar, a lokacin da suka fara jin duriyar jiragen sama a sararin samaniya, sannan jim kadan suka fara jin karar fashewar wasu abubuwa wanda daga wannan lokacin ne alamomi suk fara bayyana a jikin mutane. Duk cewa sun ce ba za su iya gane jiragen ba, amma sun san cewa jiragen Syria da na Rasha duk sun taba kai harin a wajen.

Tuni dai Rasha ta musanta cewa tana da hannu a kai harin, inda ta ce babu wani hari da ta kai a ranar Talata da ake magana. 

Hakanan ita ma gwamnatin Syria tad ade tana musanta cewa tana amfani da irin wannan makami, duk da cewa sau uku binciken Majalisar dinkin Duniya ta kama da laifin amfani da makamin.

Yadda makamin ke janyo amai da suma

An kawo harin ne ta sama, kamar yadda wakilin Majalisar dinkin Duniya Staffan de Mistura ya ce ya sanar a taron kara wa juna sani na duniya day a gudana a birnin Brussels, wanda aka shirya domin zaman lafiya.

Wata babban jami’ar Tarayyar Turai Federica Mogherini ta ce, “Lallai akwai hannun gwamnati domin kuwa hakkin ta ne ta kare rayuwar al’ummarta.” 

Wakilin Al Jazeera, Alan Fisher wanda ya ruwaito dada Beirut ana tunanin wadanda suka mutu za su karu, sannan kuma mafi yawan wadanda suka ji kanann yara ne.

“Mutane suna da suma, wasu na amai suna fitar da kunfa daga bakinsu,” inji Fisher.

“A irin wannan yanayi, ana ta kokari ne kawai a san yadda za a iya cira sinadaren a jikinsu cikin gaggawa. Amma kuma ko a hutunan da ake yadawa a kafofin sadarwa sun nuna yadda kananan yara suke kokarin yin numfashi amma abin ke gagararsu. Wasu a nan take suka mutu bayan sunfadi.”

Shugaban Syria da magoya bayansa ne suka da alhakin wannan hari- Theresa May

Firay Ministar Birtaniya, Theresa May ta ce Shugaban kasar Syria da magoya bayansa irinsu Rasha ne ke da alhakin kai wannan hari, kuma dole a tambayesu. 

May wadda ta yi wannan jawabin a lokacin da ta kai ziyara kasar Denmark, ta yi Allah wadai da wanan mummunar harin da aka kai wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki har da kananan yara, sannan ta ce ta bi sahun sauran takwarorinta na duniya wajen daukan mataki, duk da cewa ba ta fadi irin matakin da za su dauka ba.