Kamfanin mai na kasar Saudiyya, Aramco ya gano wasu sabbin riyoyin mai guda hudu a kasar.
Ministan Makamashi na Saudiyya, Yarima Abdulaziz Bin Salman, ya ce an gano rijiyoyin man ne a yankunan Reeshe da kuma As- Sarrah.
- An kashe basarake mako daya bayan garkuwa da shi a Neja
- Gawuna ya wakilci gwamnatin Kano wurin yi wa Kwankwaso ta’aziyya
- Yadda mai shayi ya zama dan Majalisa a Kano
Rijiyar mai ta farko na iya samar da iskan gas da yawansa ya kai ‘Cubic feet’ miliyan 3.2 da kuma danyen mai ganga 4,452 a kullum.
Ministan ya kara da ce a rijiyar mai ta biyu da aka haka, za a samu gangar danyen mai 2,745 da kuma iskar gas ‘cubic feet’ miliyan uku a kullum.
Ta uku kuma za ta rika samar da ganga 3,654 na danyen mai, sai kuma gas ‘cubic feet’ miliyan 1.6.
Rijiyar mai ta hudun kuma za ta ba da ‘cubic feet’ miliyan 32 na iskar gas da kuma gangar danyen mai 92 a kowace rana.
Ministan ya ce gano sabbin rijiyoyin man ya nuna irin arzikin da Allah Ya huwace wa Saudiyya kuma zai taimaka wajen samar da karin mai da iskar gas da kuma fadada kamfanin Aramco.