✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gutsure kunnen wani mai goyon bayan Ingila

Wani dan Ingila ya rasa wani bangare na kunnensa a lokacin da yake kallon gasar cin kofin duniya a tsakanin kasarsa da ta Uruguay a…

Wani dan Ingila ya rasa wani bangare na kunnensa a lokacin da yake kallon gasar cin kofin duniya a tsakanin kasarsa da ta Uruguay a makon jiya.
Kamar yadda kafar sadarwar Sunday People ta Ingila ta fitar a faifan bidiyo an nuna yadda wani mai goyon bayan Ingila ya kama kunnen dan uwansa da shi ma yake goya wa Ingila baya a gasar kuma ya gutsure wani sashe sannan ya bace a cikin dandazon ’yan kallo ba tare da an kama shi ba.
Jini ya rika kwarara a kunnen kafin likitoci su kai masa dauki.
Wannan cizo ya shafe wanda dan kwallon Uruguay Luis Suarez ya yi wa dan kwallon Italiya a makon jiya. Cizon da Suarez bai kai wannan tsanani ba, don wancan babu jini sannan kuma a baya ne.
Mutumin da aka gutsure wa kunne mai suna Robert Farkuharson ya bayyana wa ’yan jarida cewa mutumin ya gutse masa kunne ne kafin ya yi masa zagin uwa ta uba sannan ya bace a cikin dandazon mutane.  Ya ce bai san dalilin da ya sa ya aikata masa hakan ba don dukkansu suna goya wa Ingila baya ne a gasar.
Tuni jami’ar tsaro da ke kula da yankin mai suna Rachel Barber ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma ta ce rundunar ’yan sanda ta dukufa don ganin ta kamo wanda ya aikata haka. Rundunar ta ce kodayake ba a kama wanda ya aikata haka ba amma an samu sunansa al’amarin da ke nuna an kusa yin ram da shi.