✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da wani Uba da kaninsa kan zargin yi wa diyarsa fyade a Ekiti

Wata Babbar Kotun Majistire a birnin Ado-Ekiti, ta bayar da umarnin tsare wasu mutum biyu a gidan kaso bisa zarginsu da yi wa karamar yarinya…

Wata Babbar Kotun Majistire a birnin Ado-Ekiti, ta bayar da umarnin tsare wasu mutum biyu a gidan kaso bisa zarginsu da yi wa karamar yarinya ’yar shekara 14 fyade.

Jami’in dan sandan da ya gabatar da mutanen biyu, wa da kani a gaban kotun, ya ce ana tuhumar Isaac mai shekaru 48 da Ojo Obasua mai shekaru 47 kan zargin yaudara da kuma lalata da karamar yarinya.

Insfeta Johnson Okunade ya shaida wa kotun cewa, ababen zargin biyu sun aikata laifin da ake tuhumarsu da shi tun a watan Oktoban 2020 a yankun Ayegunle da ke Ekiti.

Ya ce, Isaac wanda shi ne mahaifin yarinyar ya aikata wannan laifi tare da kaninsa, wanda kuma yana cin karo da sashe na 31 cikin kundin dokokin kare hakkin yara na shekarar 2012.

Alkaliyar da ta jagoranci zaman kotun a ranar Litinin, T.O Ogunsina, ta dage sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Fabrairun 2021 kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.