Wata kotun majistare da ke titin Ibrahim Taiwo a Kaduna ta gurfanar da wasu mutane 10 da suka haɗa da kaka, bisa laifin yi wa wata nakasasshiyar yarinya ’yar shekara 16 fyaɗe a ƙauyen Likoro da ke ƙaramar hukumar Kudan ta jihar.
An ruwaito cewa wanda ake zargi mutum na 11 na hannu a lokacin da shari’ar ta taso, ranar Alhamis.
- An zaɓi Robert Prevost sabon fafaroma
- Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar Wakilai
Waɗanda ake zargin, a cewar rahoton farko da aka samu, sun ce wacce aka yi wa fyaɗen an yi ta aikat fyaɗen a lokuta daban-daban ta hanyar yaudara da kuma lallashinta ta zuwa wurarensu daban-daban inda suke da masaniya game da ita.
Lamarin ya haifar da samun ciki kuma wadda aka yi fyaɗen ta haifi ɗa namiji watanni huɗu da suka wuce.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Insfekta Yakubu I. Lemu, ya ce matakin ya saɓawa sashe na 257 na kundin laifuffuka na Jihar Kaduna.
Ya ce, “A cewar rahoton farko da aka samu a ranar 27 ga watan Oktoba, 2024 da ƙarfe 6:30 na yamma, wani Usman Yusuf ya ruwaito cewa ya gano cewa ƙanwarsa Fatima Maikanti na ɗauke da juna biyu na wata shida, ya ce a lokacin da aka tambaye ta, ta bayyana cewa a wurare daban-daban, a lokuta daban-daban waɗanda ake zargin sun yi ta lalata da ita ne, sun kai ta wurare daban-daban a ƙauyen inda ta samu juna biyu, hakan ya sa ta haifi yaro.