Wani basarake ya gurfana a gaban kotu kan keta haddin Oloba na Kasar Eju, Alhaji Maroof Afolayan Adebayo, da ke Karamar Hukumar Irepodun ta Jihar Kwara.
Basaraken Samora, Oba Matthew Idowu Ajiboye, ya gurfana a kotu ne ranar Laraba bayan shi da wasu ’yan daba sun yi wa Alhjai Maroof da iyalansa kutse tare da jikkata su.
Rahoton ’yan ya ce Oba Matthew da wasu mutum biyar dauke da muggan makamai sun yi wa Oloba da iyalansa munanan raunuka tare da kwashe musu kudade — har da na kasashen waje — a harin da suka kai musu.
Dan sanda mai gabatar da kara, Seun, ya shaida wa kotun cewa suna ci gaba da binciken lamarin, don haka ya bukaci a dage sauraron karar.
Alkalin kotu, Magistare Badmus, wanda ya saurari karar ya ba da belin wanda ake zargin a kan Naira dubu 500 da kuma mutum biyu da za su tsaya musu.
Daga nan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Satumba.