✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano kyankyaso a hanjin matashi

Bayan gano ƙwaron mai rai a cikin majiyyacin, rukunin likitocin sun yanke shawarar cire shi ta hanyar amfani da na’urar endoscope.

Likitoci a wani asibiti a birnin New Delhi na ƙasar Indiya, sun yi matuƙar kaɗuwa bayan da suka gano wani irin kyankyaso mai tsawon santimita 3 a cikin hanjin wani majiyyaci da ke ƙorafin ciwon ciki da rashin narkewar abinci.

Wani matashi mai shekara 23 ya zo asibitin Fortis, a garin Vasal Kunj kwanan nan don yin ƙorafi game da matsalolin ciki da ya shafe kusan kwanaki uku yana fama da su.

Ya koka a kan matsanancin ciwon ciki da wahalar narkewar abinci, wanda ke haifar da kumburin ciki a-kai-a-kai.

Mutumin ya ci abincin ne a kasuwar dare kwanaki kaɗan kafin nan kuma ya yi zargin cewa hakan ne ya janyo masa matsalar.

Likitoci sun yanke shawarar cewa, matakin da ya fi dacewa shi ne a gwaji da na’urar Endoscopy don gano yadda abinci ke aikin a cikinsa, da nufin gano dalilin ciwon da ke damun nasa. Abin da ba su yi tsammani ba shi ne gano wani kyankyaso mai rai a cikin ƙaramar hanjinsa.

“A cikin kwanaki biyu da suka gabata, majiyyacin ya yi fama da rashin narkewar abinci da kumburin ciki bayan ya ci abinci.

“A lokacin bincike na yau da kullun ne muka gano kyankyaso kwatsam,” in ji Dakta Shubham Vatsya, wanda ƙara shaida wa jaridar Indian Express cewa, “ko mu ma mun yi mamakin yadda kyankyaso ya ci gaba da kasancewa a cikin.”

Bayan gano ƙwaron mai rai a cikin majiyyacin, rukunin likitocin sun yanke shawarar cire shi ta hanyar amfani da na’urar endoscope.

Dakta Vatsya ya bayyana cewa, “mun kunna maɓallin tsotsa a kan iyakar na’urar, yadda ya kamata a tsotse kyankyason a cikin, wanda ya kai ga cire shi daga cikin tare da ceton rayuwar mutumin,” in ji Dokta Vatsya, wanda ya ƙara da cewa rashin cire ƙwaron da sauri zai iya yin wuya. Ya haifar masa da matsaloli, ciki har da cututtuka masu yaɗuwa.”

Dangane  da yadda kyankyaso  mai  tsayin 3cm ya shiga cikin hanjin matashin, masanin ilimin gastroenterologist na Indiya ya yi hasashen cewa zai iya kasancewa ya shiga ta maƙogwaronsa yayin da yake barci, ko kuma mutumin ya haɗiye shi lokacin da ya ziyarci kasuwar dare.