Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya yi wa Shugaba Buhari bayani kan batun yara ’yan Makarantar Sakandaren gwamnati da aka sace a Kankara, Jihar Katsina.
Gwamna Masari, ya gana da Shugaban Kasar a mahaifarsa da ke garin Daura, bisa rakiyar mataimakin gwamnan jihar, Manir Yakubu.
- Yadda na kubuta daga hannun ’yan bindiga —Dalibin GSSS Kankara
- Sace dalibai: Ya kamata gwamnati ta muttsuke ’yan ta’adda
- Amurka ta cire Sudan daga jerin kasashe masu taimaka wa ta’addanci
A wani sako da ya aike, Hadimin Shugaban Kasa a Kafofin Watsa Labarai, Garba Shehu, ya tabbatar da irin nasarar da ake samu wurin kwato yara daliban da aka yi garkuwa da su.
“Muna iya kokarinmu kuma muna ganin alamun nasara”, inji Gwamnan, kamar yadda sanarwar ta ambato yana cewa.
Gwamnan ya yi wa manema labarai karin haske dangane da ganawar ta su ta awa daya da Shugaban Kasar da suka fara tattaunawa da misalin karfe 2 na rana.
Ya ce masu garkuwar tuni sun fara tuntuba an kuma fara tattaunawa kan yadda za a tseratar da yaran su koma gida lafiya.
Masari, ya ce jami’an tsaro daban-daban sun gano inda daliban suke a halin yanzu, kuma Shugaban kasa ya himmatu ainun kan ganin an tseratar da ’yan makarantar.
Gwamnan ya ce ya kai wa shugaban kasar ziyarar ne don yi masa cikakken bayani kan lamarin da kokarin da ake na ganin an kubutar da su.