Rahotanni daga yankin Abua da ke Karamar hukumar Abua/Odual ta Jihar Ribas na cewa, an gano gawar wasu sojojin Najeriya hudu tare da wasu biyu da aka raunata da harbin bindiga a ranar Litinin.
Hakan ya faru ne bayan kai wa wata motar ma’aikatar mai hari a hanyarta na zuwa garin Omelema duk a yankin da suka kai wa sojojin harin.
- An sake kashe biyu daga cikin daliban jami’ar da aka sace a Kaduna
- Yadda aka yi jana’izar Mahaifiyar Sarkin Kano
Kisan sojojin na zuwa ne kimanin awanni 24 bayan kai wani hari da wasu da ake zargin ‘Yan awaren Biyafara (IPOB) ne suka kai kan wasu jami’an tsaro yayin da suke bakin aiki a yankin Omagwa da yankin Isiokpo na Karamar Hukumar Ikwerre da ke Jihar.
Wannan mummunan hari ya kai ga kisan wasu jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda da kuma wani jami’in Kwastam daya.
Aminiya ta gano cewa, an kai wa sojojin harin ne yayin da suke gadin wasu Ma’aikatan wani kamfanin mai da ke garin Omelema a safiyar ranar Litinin kafin su yi garkuwa da Ma’aikatan kamfanin.
Wata majiya daga mazauna yankin da abun ya faru ta ce, ‘yan bindigar sun kai wa motar Ma’aikatan kamfanin samar da man harin ne a daidai lokacin da suke kokarin kai mai zuwa wani gidan mai da ke yankin.
An yi kokarin kokarin tuntubar Kakakin rundunar Sojin Najeriya na ofishin shiyya ta shida da ke Fatakwal, babban birnin Jihar, Major Charles Ekeocha amma bai daga kiran waya ko amsa sakon da aka tura masa ba kan faruwar lamarin.
Yayin da aka tuntubi Kakakin rundunar ‘Yan sanda na Jihar Ribas, Nnmadi Omoni ya ce, suna da masaniya kan lamarin amma basu da cikakken bayanin a kai.