An gano gwawar mutum 15 a yayin da ake ci gaba neman wasu uku bayan hastarin kwalekwale da ya auku a yankin Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.
Kwalekwalen ya kife ne a yayin da yake ɗauke da mutum 43 da buhuna 60 na shansherar shinkafa da shanu uku da tumaki biyu a ranar Asabar.
Kifewar kwalekwalen ta auku ne a sakamakon karonsa da wani kututture bayan ya ɗauki fasinjojin daga yankin Guni zai kai su kasuwar mako-mako da ke yankin Zumba da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro.
Manajan Hukumar Albarkatun Koguna ta Ƙasa (NIWA), mai kula da yankin, Akapo Adeboye, ya ce an gano gwawar mutum 15, amma ana ci gaba neman wasu mutum uku, ko da yake cewa an yi nasarar ceto mutum 26 da ke sanye da rigunan kariya da ransu, bayan aukuwar hatsarin.
- HOTUNA: Yadda Aisha ta koma gidan Buhari na Kaduna
- NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INEC
Adebayo ya bayyana cewa, “Mutanen sun taso ne daga ƙauyen Shayita za su tafi Kasuwar Kwata da ke Zumba tare da kayansu na miliyoyin kuɗaɗe a ranar Asabar 26 ga watan Yuli, 2025.
“Jami’an NIWA sun gudanar da aikin ceto, amma an samu asarar rayuka 18, an ceto wasu 26, kuma aka ci gaba da aiki da kuma ƙoƙarin kamo mai kwalekwalen.”
Shaidu sun ce hastarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na ranar Asabar, kuma yawancin fasinjojin mata ne da ƙananan yara, kuma jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) sun tabbatar da hakan.
Sarkin Ruwan Zumba, Umar Isah, ya ce mutum 15 ne suka rasu, an ceto 25, amma an yi asarar shanu uku da buhu 60 na shansherar shinkafa.
“A cikin mutum 15 da suka rasu har da ƙananan yara uku mata da gano gawarwakinsu,” in ji shi.
Amma Darakta Janar na Hukumar NSEMA, Abdullahi Baba Arah, ya ce gawa 13 aka gano kuma an yi jana’izarsu a ranar Lahadi.
Arah, wanda ya tabbatar da asarar wasu mutane da dabbobi da kayan abinci a hatsarin, ya ce gawarwakin sun haɗa da mata takwas da maza uku da kuma yara biyu.