Masu aikin ceto sun gano gawarwakin mutum 10 da suka nutse bayan kwalekwale da suka shiga domin guje wa ’yan bindiga da suka kai musu hari ya kife a Jihar Zamfara.
Mazauna kauyukan Birnin Waje da Zauma a Karamar Hukumar Bukkuyum ta jihar sun shaida wa Aminiya cewa masu aikin ceton da suka tura ne suka gano gawarwakin bayan hatsarin kwalekwale ranar Laraba da dare.
An kuma gano wasu gawarwaki uku suna yawo a wani kogi kusa da kauyen Nasarawar Kifi a Karamar Hukumar Gummi da ke makwabtaka da Bukkuyum.
“Mazauna unguwar sun kira ne domin su sanar da mu cigaban da aka samu kuma mun ba su izinin daukar hotunan gawarwakin wadanda abin ya yi ajalin su, sannan su binne su a can.
“Kimanin mutane 10 ne har yanzu ba a gan su ba, yayin da ake ci gaba da neman karin gawarwaki, duk da cewa an samu ruwan sama a yankin.
“An yi imanin cewa wani jagoran ’yan bindiga mai suna Buzu ne ya kai harin, kasancewar ya dade yana addabar al’ummar karamar hukumar tare da korar da yawa daga cikinsu.
“A harin na jiya (Laraba), ya yi garkuwa da mutane kusan 20, wadanda ya kai su cikin azuzuwan wata makarantar firamare da aka yi watsi da ita a Nannarki, kauyen da ya kori mutane, mai nisan kilomita 10 Gabas da titin Anka zuwa Gummi.
“Ya mayar da makarantar firamaren da aka yi watsi da ita sansaninsa, yana kai duk wanda ya yi garkuwa da shi can kuma yakan nemi mutane su kai kudin fansar ’yan uwansu da ya kama a can.
“Duk mai son haduwa da shi, a can yake samun shi,” in ji Babangida Bukkuyum.
Da aka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya yi alkawarin zai waiwayi wakilinmu daga baya.
Ya ce wa wakilin namu, “Ba ni minti 15 zan neme ka,” amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin da aka kammala rubuta labarin.
Shi ma da aka tuntube shi, Babban Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Zamfara (ZEMA), Mustapha Ahmad Gummi, ya ce har yanzu ba a sanar da hukumar faruwar lamarin a hukumance ba.
A cikin makonnin da suka gabata, al’ummomin yankin sun sami karuwar hare-hare masu muni.
Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton suna boye a cikin dazuzzukan Gando da Barikin Daji da ke kananan hukumomin Bukkuyum da Gummi ne ke kai hare-haren.
Mako biyu da suka gabata wasu ’yan bindiga sun harbe wasu mutum 15 da ke Sallah a wani masallaci da ke unguwar Ruwan Jema a Karamar Hukumar Bukkuyum.