An gano wani abu da ake zargin bom ne a makarantar firamareta ta Afara Unity da ke Karamar Hukumar Umuahia, Jihar Abia a yayin a dalibai ke shirin daukar darussa.
Da Ganin abin fashewan da ake zargi a ranar Alhamis, nan take aka umarci dalibai da malamai su koma gidajensu, yayin da Sashen ’Yan Sanda Masu Kwance Ababen Fashewa (EOD) ya dukufa aiki da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
- Dalibi ya yi dogon suma bayan yi masa bulala 6,000 a Ilorin
- Damfarar N450m: Kiristoci sun fi Musulmi tausayi —Ummi Zee-zee
- Matashi ya fille kan kakarsa ya kai ofishin ’yan sanda
“Muna jiran rahoton jami’an Sashen EOD na ’yan sanda da ke bincike kan lamarin,” inji Kwamishinan Yada Labarai da Dabaru da Jihar Abiya, John Okiyi Kalu a zantawarsa da Aminiya.
Bom din da ake zargi na da alamun tsatsa a jikinsa, abin da ya sa ake zargin ragowar bama-baman da aka yi amfani da su a Yakin Basasan Najeriya ne.
Kwamishin ya ce a halin yanzu an dauki matakan tabbatar da kariyar dalibai da malamai, yayin da Gwamna Okezie Ikpeazu ya umarci hukumomin tsaro su dauki matakan dakile duk wata baraza a wuraren da ke cikin hadari.