✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fitar  da jadawalin Zakarun Turai

A ranar Litinin da ta gabata ce Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) ta fitar da Jadawalin Gasar Zakarun Turai. Jadawalin ya nuna yadda aka…

A ranar Litinin da ta gabata ce Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) ta fitar da Jadawalin Gasar Zakarun Turai.

Jadawalin ya nuna yadda aka kasafta kungiyoyi 16 wajen fafatawa da junansu don a samu wadanda za su haye zuwa mataki na gaba. Wasannin za su gudana ne a gida da waje kafin a samu wadanda za su haye mataki na gaba.

Jadawalin ya nuna za a fara wasannin zagayen farko ne a tsakanin ranakun 18 da 19 ga watan Fabrairun badi, yayin da za a yi wasannin zagaye na biyu a ranakun 10 da 11 da  17 da 18 ga watan Maris din badi.  Daga nan ne kungiyoyi 8 za su kai matakin kusa da na karshe wato Kwata-Fainal.

Idan za a tuna kulob din Liberpool da ke Ingila ne yake rike da kofin sannan yana daga cikin kungiyoyin da suka kai wannan matsayi.