A ranar Litinin da ta wuce ne Hukumar shirya kwallo a Nahiyar Afirka watau CAF ta fitar da jadawalin gasar cikin kofin zakarun kulob-kulob na Nahiyar da aka fi sani da CAF Champions League.
An gudanar da bikin jadawalin ne a Marrakech da ke kasar Maroko.
Kulob din Kano Pillars zai hadu ne da na AS bita da ke Dimokuradiyyar Kongo yayin da kulob din Enyimba da ke Aba zai gwada kwanji da kulob din Anges De Notse na Togo.
Za a fara buga wasannin farko a tsakanin ranakun 7 zuwa 9 ga Fabrairun shekara mai zuwa ne yayin da za a yi wasa zagaye na biyu a tsakanin ranakun 14 zuwa 16 ga watan Fabrairun.
Kano Pillars ce ta zama zakara a gasar rukuni-rukuni na Najeriya a kakar wasan da ta wuce yayin da kulob din Enyimba ya kasance na biyu.
An fitar da jadawalin gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Nahiyar Afirka
A ranar Litinin da ta wuce ne Hukumar shirya kwallo a Nahiyar Afirka watau CAF ta fitar da jadawalin gasar cikin kofin zakarun kulob-kulob na…
