✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An fille kan mutum a sabon rikici a Filato

Fulani da ’yan kabilar Irigwe na zargin juna da kai sabbin kashe-kashen.

An kashe akalla mutum uku ciki har da wani wanda aka fille wa kai a wasu sabbin hare-hare da aka kai a Jihar Filato.

Aminiya ta gano cewa an kai hare-haren ne a lokuta daban-daban a wasu kauyuka biyu na Karamar Hukumar Bassa ta jihar.

Harin na farko an kai shi ne a unguwar Kwachudu inda aka fille wa wani Bafulatani makiyayi kai.

Shugaban Kungiyar Maikiyata ta Miyetti Allah, Reshen Jihar Filato, Nura Abdullallhi, ya yi zargi ’yan kabilar Irigwe da fille kan wani makiyayi mai suna Musa Sale tare da raunata wani mai suna Abdulsalam Nuhu a lokacin da suka je kiwo a yankin Kwachudu a ranar Lahadi.

Sai dai kuma al’ummar kabilar ta Irigwe da ake zargi da hannu a harin sun musanta zagin a matsayin mara tushe.

A safiyar Litinin ne kuma aka kashe wasu mutum biyu ’yan kabilar Irigwe a yankin Renwienku da ke karamar hukumar ta Bassa.

Mai magana da yawun Kungiyar Cigaban ’Yan Kabilar Irigwe, Malison David, ya zargi Fulani da kai harin, amma Fulani sun nesanta kansu da harin.

An kai wadannan sabbin hare-haren ne kimanin kwana biyar bayan bangarorin biyu sun yi wata tattaunawar zaman lafiya tare da Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sanda na Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, game da lamarin, amma bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da wakilinmu ya tura masa ba.