Ana zargin ’yan Bijilan da fasa idon wata amarya mai suna Khadija Abdullahi, lokacin da ake tsaka da bikinta a garin Dantamashe da ke Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano.
Lamarin dai ya faru ne a karshen makon da ya gabata, inda aka fasa mata ido daya, a daidai lokacin da ya kamata a ce ana shirin kai ta dakin mijinta.
- DAGA LARABA: Alakar ’yan aiki da iyayen gidansu: A ina gizo ke saka?
- Yadda gidan talabijin a Turkiyya ya kwashe ma’aikatan BBC Hausa guda 9
A cewar shaidun gani da ido, an gayyato ’yan Bijilan din ne domin su hana taron fatin da ake yi, wanda amaryar ta shirya.
Sai dai lamarin ya rikide ya zama tarzoma, inda aka rika jifa da duwatsu, har daya daga cikinsu ya sami amaryar a ido.
Wasu majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa ’yan unguwar ne suka gayyato ’yan Bijilan din domin su tarwatsa taron, bayan hana irinsa kwata-kwata da dattawan unguwar suka yi.
Ita ma da take tsokaci a kan lamarin, amarya Khadija ta ce ba za ta iya tuna lokacin da mutanen suka isa wajen ba, kawai ta farka ne ta gan ta a gadon asibiti.
Ta ce, “Muna tsaka da bikinmu ne kawai sai na ga ’yan Bijilan din su sun taho, kimanin su 10, suna dukan mutane suna cewa ba za a yi fatin ba.
“Daga nan ban san me ya faru ba, kawai na farka na gan ni kwance a gadon asibiti da fasasshen idanu ne,” in ji ta.
Shi ma angon Khadija, Hamisu Bala, ya bayyana lamarin a matsayin wani yunkuri na lalata musu farin cikinsu da gangan, inda ya yi kira ga hukumomi da su kwato wa amaryar tasa hakkinta.
To sai dai ’yan Bijilan din sun nesanta kansu daga zargin aika-aikar, inda suka ce sabanin tsakanin ’yan unguwar ne da kwamitin da ya hana shagalin.
A cewar Kwamandan rundunar a Karamar Hukumar, Naziru Abubakar Adamu, “Babu abin da muka yi a wajen, yanzu haka maganar da muke da kai muna ofishin ’yan sanda tare da duk mutanen da lamarin ya shafa.”
To sai dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Kano ta ce tuni ta cafke mutum biyu a kan lamarin, kuma za ta tisa keyar su zuwa kotu da zarar ya kammala bincike.