✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara zawarcin ’yan wasa a Turai

Nottingham Forest na fuskantar yanayin da dole ta sayar da ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasanta.

Bayan rufe hada-hadar kasuwar ’yan wasan kwallo kafa a Turai a Disamban bara ce aka fara mayar da hankali a kan kasuwancin ’yan wasa na watan Yunin bana.

Kasuwar ’yan wasa ta watan Yuni ta fi zafi kasancewar lokacin ne ake komawa sabuwar kakar wasanni, inda kowane dan wasa ke da ikon taka kowane irin wasa na kowace gasa.

Tuni magana ta kare game da makomar dan kwallon Faransa Kylian Mbappe, hakan ya sa Aminiya ta kalato wasu fitattun ’yan wasan da ake tunanin za su baje kolin kasuwancinsu a bana kamar yadda BBC ya ruwaito.

Ɗaya daga cikin masu Kungiyar Manchester United Sa Jim Ratcliffe na son a maye gurbin kocinsu Erik ten Hag da kocin Ingila Gareth Southgate.

Nan ba da jimawa ba kocin mai shekara 53 zai sanar da matsayarsa. (Star)

Manchester City na iya bai wa ɗan wasan gefe na Ingila, Jack Grealish mai shekara 28, damar barin kungiyar a wannan kaka, yayin da take ƙoƙarin haɗa kuɗin inganta kungiyar. (HITC)

Mai taka leda a Newcastle United da Sweden Aledander Isak, mai shekara 24, na cikin ’yan wasan da Arsenal ke hari a ƙoƙarin sayo ɗan wasan gaba a karshen kaka. (Football Insider)

Arsenal na kuma zawarcin dan wasan Sporting Lisbon da Sweden, Viktor Gyokeres, mai shekara 25. (Teamtalk)

Tottenham da Chelsea da West Ham na farautar ɗan wasan Ingila mai shekara 28, Ivan Toney, 28, wanda hankalinsa ke kan Brentford. (Sun)

Ɗan wasan gaba da ke kai hari a Jamus, Timo Werner mai shekara 28, na son Tottenham ta sake shiga tattaunawar saye shi na dindindin a wannan kaka, kan Yuro miliyan 17 daga kungiyarsa ta RB Leipzig. (Florian Plettenberg)

Mai buga tsakiya a Denmark Christian Eriksen, mai shekara 32, ya faɗa wa kocin Manchester United, Erik ten Hag cewa ba ya jin daɗin wasanninsu. (Tipsbladet)

Tsohon mai daukar ma’aikata a Chelsea, Scott McLachlan ya kasance wanda Newcastle ke hari don maye gurbin daraktan wasanninta, Dan Ashworth, da ke shirin tafiya Manchester United. (Teamtalk)

Rangers ta shirya karbar Fam miliyan 15 a kan mai tsaron raga na Ingila Jack Butland, mai shekara 31, yayin da yake sake samun farin jini a tsakanin ƙungiyoyin firimiya. (Football Insider)

Everton da Nottingham Forest da West Ham na harin ɗan wasan gefe a Ingila, Karamoko Dembele, mai shekara 21, wanda ya taka rawar gani a kakar bana bayan buga wasan aro a Blackpool daga Kungiyar Brest ta Faransa. (HITC)

Kalubalantar matakin kwashe mata maki hudyu da Nottingham Forest ta yi kan laifin karya dokokin kuɗaɗe na iya girmama zuwa hukunci mafi tsanani. (Times)

Nottingham Forest na fuskantar yanayin da dole ta sayar da ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasanta zuwa karshen Yuni domin guje wa yanayin da zai kai ga sake zabtare mata maki kan aikata makamancin wannan laifi a sabuwar kaka. (Times).

Ɗan wasan gaba Beljiyum Johan Bakayoko na jan hankalin kungiyoyin Chelsea da Liverpool da Manchester City da Paris St-Germain, yayin da PSV Eindhoven ke jiran akalla Yuro miliyan 50 zuwa 60 a kan matashin mai shekara 20. (Sky Sports Jamus)

Ɗan wasan Manchester City, Erling Haaland, mai shekara 23, ya daga hankalin ƙungiyarsa sakamakon fita daga filin atisaye yana ɗinginshi bayan ya je Norway domin buga wa kasarsa wasan sada zumunta. (Guardian)