✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara yi wa maniyyata aikin Hajji rigakafin COVID-19

Sau biyu za a yi wa maniyya aikin Hajji rigakafin kafin su tafi Kasa Mai Tsarki

An fara yi wa maniyyata aikin Hajjin bana allurar rigakafin cutar COVID-19 a Jihar Kwara.

Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara ta kaddamar da aikin rigakafin ga maniyyatanta 2,500 ne a ranar Juma’a a shirye-shiryen farar tafiyarsu Kasa Mai Tsarki domin sauke farali.

Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko na Jihar wadda ke gudanar da aikin, Alhaji AbdulGaniyu Ahmed ya ce, “Rigakafin da ke wa maniyyata na daga cikin sharuddan da Gwamnatin Saudiyya ta shimfida na samun izinin shiga kasarta.

“Za a yi rigakafin annobar COVID-19 na biyu bayan mako shida da yin na fakro”.

Ya kara da cewa bayan rigakafin COVID-19, za kuma a yi wa maniyyata rigakafin da aka saba a baya.

Don haka ya shawarci maniyyata daga Kananan Hukumomi 16 na Jihar da su gabatar da kawunansu a yi musu allurar rigakafin, a ba su takardun shaida.

A nashi bangaren, Shugaban Hukumar Alhazan Jihar, Sambo Sambaki ya ce ana sa ran daukacin maniyyatan za su karbi allurar rigakafin kafin a fara tafiya Kasa Mai Tsarki sauke farali.

Jami’ar Kula da Rigakafi a Hukumar Lafiyar, Sarat Yoonusu ta ce yin allurar wani mataki ne na hana bazuwar cutar COVID-19, ta kuma ba da tabbacin cewa allurar ba ta da wata illa kamar yadda ake rade-radi.

Wasu daga maniyyatan da aka yi wa allurar, Mopelola Kadir da Asiata Amope sun yaba wa hangen nesan gwamnatin jihar wurin kokarin hana bazuwar cutar a jihar.