Maniyyata sun fara shiga birnin Makkah na kasar Saudiyya domin fara shirye-shiryen ibadar Aikin Hajjin bana.
Wannan dai shine karo na biyu da ake takaita yawan masu gudanar da ibadar saboda kaucewa yaduwar annobar COVID-19.
- Ya jagoranci kai farmaki kayukan Zamfara saboda kama mahaifinsa
- An kama boka da kokon kan mutum a Kuros Riba
A bana dai mutum 60,000 wadanda aka yi wa cikakkiyar rigakafin cutar kuma mazauna kasar ne za a kyale su yi aikin, cikin fatan da take yi na ganin cewa an sami nasarar rashin samun wanda ya kamu da ita kamar a bara.
A bana dai an zabi mutanen da zasu gudanar da ibadar ne ta hanyar yin kuri’a, yayin da Musulmai da dama daga kasashen waje aka sake haramta musu zuwa.
Bayan dibarsu a manyan motocin safa-safa, an kai maniyyatan Masallacin Harami, tuni suka fara Dawafi a dakin Ka’aba.
Mafi yawa daga cikinsu dai suna amfani da laima don kare kansu daga zafin rana.
“Duk bayan sa’a uku, mutum 6,000 suna shiga su yi Dawafi idan suka zo,” kamar yadda Kakakin Ma’aikatar Aikin Hajjin Saudiyya ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
Aikin Hajji dai na daya daga cikin ibadu mafi tara mutane masu yawa a duniya, inda ko a 2019 mahajjata miliyan biyu da rabi ne suka gudanar da aikin.
Ibadar kuma na daya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar da ake bukatar kowanne Musulmi mai hali ya yi, akalla sau daya a rayuwarsa.
An tsaurara matakan kariya a bana
An dai zabi mutum 60,000 din ne daga cikin kimanin 558,000 da suka nemi gudanar da aikin bayan yin kuri’a, kuma wadanda aka yi wa cikakkiyar rigakafin ’yan tsakanin shekara 18 zuwa 65 ne kawai za su yi aikin.
“An raba maniyyatan ne zuwa rukuni-rukuni, inda kowanne rukuni ya kunshi mutum 20 kacal, domin takaita yawan cudanyar mutane,” inji Mohammed Albijawi, Sakataren Ma’aikatar Aikin Hajjin.
Ya zuwa yanzu dai, sama da mutum 507,000 ne suka kamu da cutar a kasar inda 8,000 daga ciki kuma suka rasu.
An kuma yi wa sama da mutum miliyan 20 rigakafi a kasar da take da mutane miliyan 34.
Aikin Hajjin bara dai na daya daga cikin mafiya karancin mutane da aka taba gudanarwa a cikin shekaru masu yawa, inda mutum 10,000 ne kacal suka yi ibadar.
Ba a dai samu rahoton kamuwa da cutar a sanadiyyar aikin ba a bara, kasancewar hukumomi sun dauki matakan kariya iri-iri.
Babban kalubalen aikin a bana dai shine yadda za a kammala ibadar ba tare da an sami sabbin kamuwa da cutar ba. (AFP).