✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara rububin yayan Paul Pogba a gasar firimiya

Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun nuna kulob din Tottenham da na Sunderland sun fara rububi a kan yayan Paul Pogba.  Paul Pogba wanda…

Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun nuna kulob din Tottenham da na Sunderland sun fara rububi a kan yayan Paul Pogba.  
Paul Pogba wanda ya kafa sabon tarihi a matsayin dan kwallo mafi tsada a duniya tun bayan da ya canza sheka daga kulob din Jubentus na Italiya zuwa na Manchester United a watan jiya, an ruwaito dan uwansa mai suna Florentin Pogba mai kimanin shekara 26  akwai yiwuwar ya koma Ingila don ya cigaba da yin kwallo.
Kafar sadarwa ta The Sun ta kalato cewa tsohon kocin Manchester United da Eberton da yanzu haka yake horar da kulob din Sunderland Dabid Moyes ya taya Floretin a kan Dala miliyan 8.5.  Haka labarin ya nuna shi ma kulob din Tottenham ya nuna bukatarsa a kan dan kwallon.
Shi dai Florentin Pogba yana buga kwallo ne a baya a kulob din St. Etieine na Faransa kuma Sundarland ta nuna tana son ya maye gurbin dan kwallonta mai suna Lamine Kone wanda yake yunkurin barin kulob din.
Shi dai Yayan na Pogba ya fara yi wa kulob din St. Etienne na Faransa kwallo ne tun daga shekarar 2012 bayan an yaye shi daga kulob din matasa a kulob din.
Idan cinikin ya kaya, akwai yiwuwar ’yan kwallon su fuskanci juna a gasar firimiya, a lokacin da Manchester United za ta hadu da ta Sunderland.