Ya zuwa wannan lokaci kulob da dama da ke kasar Afirka ta Kudu da kuma wasu da ke yankin Turai ne suka fara yunkurin dauke dan kwallon gaba a kungiyar Super Eagles ta Najeriya mai wsuna Ejike Uzoenyi saboda haskakawar da ya yi a gasar cin kofin Afirka da yanzu haka take gudana a Afirka ta Kudu.
Rahotannin da kafofin watsa labarin wasanni sun nuna kulob da dama da ke Afirka ta Kudu da kuma sassan duniya ne suka fara rububin dan kwallon jim kadan bayan Najeriya ta lallasa Maroko da ci 4 da 3 a wasan kusa da na karshe Kwata-Fainal a karshen makon jiya.
Sai dai dan kwallon ya ki ba su kai don bori ya hau inda ya nemi su dakata har sai bayan an kammala gasar a jibi Lahadi.
“Saboda ba na son raba hankalina biyu ne ta sa na shawarce su da su tsaya har sai bayan an kammala gasar”, inji Ejike a lokacin da yake bayani ga ’yan jarida.
Ejike wanda yanzu haka yake buga wa kulob din Enugu Rangers ya ce a halin da ake ciki abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne yadda zai taimaka wa Najeriya lashe kofin Afirka rukunin masu kwallo gida a karon farko a tarihin gasar tun bayan da aka kirkirota kimanin shekara uku da suka gabata.
Idan za a iya tunawa Ejike yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles da suka yi kokari a wasansu da Maroko a lokacin da Maroko take kan gaba a wasan da ci 3-0 kafin hutun rabin lokaci amma bayan da aka dawo ne suka fanshe kwallayen kuma suka kara ta hudu da hakan ya sa Najeriya ta haye matakin semi-fainal da ci 4-3.
…An fara rububin dan kwallon Super Eagles Ejike Uzoenyi
Ya zuwa wannan lokaci kulob da dama da ke kasar Afirka ta Kudu da kuma wasu da ke yankin Turai ne suka fara yunkurin dauke…