Ukraine ta fara kwashe fararen hulanta daga birnin Sumy da ke Arewa Maso Gabashin kasar, a karkashin wata yarjejeniya da ta kulla Rasha, wadda ta bude hanyar ficewa daga biranen da dakarun Rasha suka mamaye.
A daya hannun kuma, Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya koka bisa yadda Kasashen Yamma suka gaza cika alkawarin kare kasarsa daga mamayar Rasha.
Motocin basne suke aikin kwashe fararen hular zuwa birnin Lokhvytsya, mai nisan kilomita 150 a Kudu maso Yamacin Ukraine da ke karkasin ikon dakarunta, bayan da farko gwamnatin kasar ta yi watsi da tayin kwashe mutanen zuwa Rasha.
Rasha ta sanar da tsagaita wuta a birane biyar da rikicin ya fi yin kamari, wato Chernihiv, Mariupol, Kharkiv, Kyiv da Sumy.
Ukraine ta ce mutum 21 ne aka kashe ciki har da kananan yara da mata a sumy sakamakon luguden wutar Rasha a yankin.
Bayan kwana 13 ana kai ruwa rana tsakanin Rasha da Ukraine, Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane da ke tserewa daga rikicin sun haura miliyan biyu.
Shugaba Volodymyr Zelensky ya caccaki abin da ya kira saba alkawarin kare kasarsa da Kasashen Yamma suka yi.
A yayin da ake ci gaba da rikici, Amurka ta ce ta samu rahoton da ke nuna cewa Rasha na daukar sojojin haya daga Syria, sai dai Rashar ta musanta zargin.