Ko a sahun ’yan canji Lionel Messi bai samu shiga ba yayin da Inter Miami ta yi rashin nasara a wasan karshe na gasar Kofin US Open a Yammacin Laraba.
Tuni dai mai horar da Inter Miami Gerardo Martino ya ce za su dauki kasadar doka wasan karshe na cin kofin US Open ba tare da tauraronsu Lionel Messi ba.
- Dalilin da Morocco ta yi wa Najeriya zarra a karɓar baƙuncin Gasar AFCON ta 2025
- Sakamako, jadawali da wainar da ake toyawa a Carabao Cup
Messi bai samu buga wasan ba ne saboda rauni da ya hana shi doka wasan a tsakaninsu da Houston Dynamo a daren jiya na Alhamis.
Masu sharhi kan harkokin wasanni na ganin cewa, rashin haskawar Messi ce a wasan ya sanya kungiyar da ake yi lakabi da The Herons ta sha kashi a hannun Houston Dynamo da ci 2-1.
Kawo yanzu dai Inter Miami ta samu nasara a wasanni biyu kacal cikin hudu da ta buga ba tare da Messi ba tun bayan zuwan sa kungiyar a watan Yuli, sai dai lamarin a ranar Laraba ya kara cin tura yayin da kungiyar ta rasa dan wasanta Jordi Alba saboda rauni.
A minti na 37 da fara wasa ne tsakanin Inter Miami da Orlando City aka cire Messi daga wasan saboda raunin da ya samu a ranar 20 ga watan Satumba.
A cewar kociyan Martino, Messi ya yi fami ne a kan tsohon raunin da ya samu tun kafin ya zo kungiyar amma sun yi tsammanin ya iya warwarewa kafin wasan na jiya.
Messi wanda Inter Miami ta sayo daga PSG cikin watan Yulin da ya gabata, zuwa yanzu ya zura kwallaye 11 a wasanni 12.
A ranar Asabar ne kungiyar ta The Herons za ta dawo taka leda yayin da za ta karbi bakuncin NYCFC a fafatawar gasar Eastern Conference.