A ranar Litinin da ta gabata ce dan wasan Ajantina da Inter Miami, Lionel Messi ya sake lashe kambin Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya (Ballon d’Or) karo na 8.
Dan wasan ya karbi kambin ne a wani biki da aka yi a birnin Paris na Faransa, kamar yadda aka saba yi duk shekara.
- Mawakan siyasa da suka yi nadamar yi wa Buhari waka
- Ana zargin mai unguwa da fyade da sa wa yarinya cutar HIV a Jigawa
Mai shekara 36, Messi ya karbi kambin ne daga daga hannun Karim Benzema wanda shi ne mai rike da kambin na bara, bisa la’akari da kwazon da ya nuna, musamman na jagorantar kasarsa ta Ajantina wajen lashe Gasar Cin Kofin Duniya da aka yi a kasar Katar.
Dan wasan Manchester City, Erling Haaland ne ya zo na biyu, yayin da Kylian Mbappe na Kungiyar PSG ya zo na uku, Kevin De Bruyne kuma ya zo na hudu.
Messi ya lashe kambin na farko ne a shekarar 2009, sannan daga lokacin zuwa yanzu, ya lashe sau takwas ke nan, tarihin da masu bibiyar harkokin kwallon kafa suke tunanin zai yi wahalar gaske a iya karyawa, ko kuma za a dauki tsawon lokaci kafin a karya.
Sai dai lamarin ya bar baya da kura, inda wasu suke ganin Haaland, wanda ya jagoranci Kungiyar Manchester City wajen lashe kofi uku, ciki har da Kofin Zakarun Turai ne ya cancanci kambin, wasu kuma na ganin Kylian Mbappe, wanda ko a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniyar ya fi Messi taka leda, inda ya zura kwallo uku rigis a ragar Ajantina.
Mbappe dai ya zura kwallo takwas ne a gasar, inda a karshe ya tashi a matsayin wanda ya fi zura kwallaye a gasar.
Haaland ya yi matukar jan zarensa a kakarsa ta farko a Gasar Firimiya ta Ingila bayan zuwansa kungiyar daga Borussia Dormund a watan Yunin 2022.
Dan kasar Norway ya zura kwallo 36 a wasa Firimiya 35, sannan ya tashi da kwallo 42 a wasa 53 a dukkan gasannin da ya buga.
Messi ya kare kwallo a Kungiyar PSG ne da kwallo 21, sannan ya taimaka aka ci guda 16. Haaland ya lashe kofi uku; Zakarun Turai da Kofin Kalubale (FA) da Firimiyar Ingila.
Shi kuma Messi ya ci kofin Faransa ne da Kofin Duniya.
Sai dai a daidai lokacin da wasu ke korafin cewa an danne hakkin Haaland, masu sharhi a harkokin wasanni sun ce a Gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 2006 da Italiya ta lashe, dan wasan bayanta Cannabaro ne ya lashe kambin Ballon d’Or a shekarar saboda bajintar da ya nuna a gasar.
An dade ana tafka muhawara a kan tsakanin Ronaldo da Messi wa ya fi wani, inda ake amfani da kalmar GOAT wato Greatest of all time wajen bayyana wanda ya fi.
Amma ba ko tantama a kan su biyun suna gaba da kowa, domin an kasa samun wanda zai dusashe tauraronsu har ta kai ana tunanin ba a taba samun ’yan wasa ba kamar su a tarihin tamaula.
A baya, an yi zaratan ’yan wasa, tun lokacin su Johan Cruyff da Pele da Michael Platini da Mardona da sauran takwarorinsu.
Har zuwa lokacin su Zinedine Zidane da su Ronaldo na Brazil da Figo da Rivaldo da suransu.
Amma a tarihin kwallo ba a taba samun wadanda suka dade suna zamani ba kamar Ronaldo da Messi musamman a shekara goma sha zuwa 20 da suka gabata domin da wuya ka ga dan kwallo ya yi shekara 10 tauraronsa bai dusashe ba, amma su abin kara gaba ya rika yi.
Sai a kakar bara da aka fara ganin alamar sun fara yin kasa.
Ronaldo ya bar Kungiyar Manchester United ya koma Kungiyar Al Nassr ta Saudiyya, inda duk da cewa yanzu na jan zarensa a gasar kasar, ana ganin alamar sanyi domin bai kamata ya koma taka leda a wajen Turai ba.
Haka kuma rahotanni sun nuna cewa sai dai ya rasa babbar kungiyar da za ta dauke shi ne ya yanke shawarar tafiya Saudiyya.
A bangaren Messi, duk da ya lashe Gasar Kofin Duniya da Ajantina, ana ganin komawarsa Kungiyar PSG ta Faransa bai haifar da da mai ido ba.
Sai dai a dadai lokacin da ake tunanin sun yi sanyi, sai Messin ya sake lashe Ballon d’Or karo na takwas, ya doke Haaland da Mbappe, sannan shi ma Ronaldo ya kama hanyar samun kwallo 1,000.
’Yan wasan da Ronaldo da Messi suka hana tashe
Daga cikin wadanda tashen Ronaldo da Messi ya danne su, inda suka kasa lashe kyautar gwarzon dan kwallo duk da sun kware akwai Xabi da Iniesta da Suarez da Torres da Buffon da Ribery da sauransu.
Shi kansa Kaka, ba don Ronaldo da Messi ba da ya lashe sama da daya.
Akwai kuma irin su Neymar da Griezman da suma suka nuna kwarewa, amma yanzu shekarunsu sun ja, har sun fara tunanin ritaya, alhalin su Messi da Ronaldo suna cigaba da taka leda.
Aminiya ta ruwaito yadda Hazard, wanda aka yi tunanin zai iya maye gurbin zaratan ’yan wasan ya yi karkon kifi, inda tuni ya yi ritaya ya koma gefe.
Yanzu kuma zararan ’yan wasan da duniya take yayi, su ne Haaland da Mbappe, amma su ma har yanzu Ronaldo da Messin suna gogayya da su.
Sannan akwai Jude Bellingham da shi ma yanzu tauraraonsa ya fara haske.
Shin Osimhen zai lashe kambin Gwarzon Dan Kwallon Afirka?
A jerin gwarazan ’yan kwallon kafa na bana, dan wasan Nijeriya Victor Osimhen, ya kafa tarihi na shiga cikin zaratan ’yan kwallon duniya guda 10.
Osimhen ne ya zo na 8 a duniya, inda ya zama na farko a Afirka a gaban Salah da Onana da sauransu.
Hakan ya sa ake tunanin shi ne zai zama Gwarzon Dan Kwallon Afirka