✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Morocco ta yi wa Najeriya zarra a karɓar baƙuncin Gasar AFCON ta 2025

Morocco na tutiya da manyan filayen wasa na-gani-na-fada da dama.

Takarar hadin gwiwa da Najeriya ta yi tare da jamhuriyar Benin ba ta haifar da da mai ido ba a yayin da Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika CAF ta bayyana Morocco a matsayin kasar da za ta karbi bakuncin Gasar Kofin Nahiyar Afrika (AFCON) ta 2025.

Wannan rashin sa’a da Najeriya ta yi na zuwa ne kuma a daidai lokacin da aka aka bayyana sunan kasashen Kenya da Uganda da Tanzania a matsayin kasashe 3 da za su yi tarayya wajen karbar bakuncin gasar ta 2027.

Rabon da Najeriya ta samu damar daukar nauyin gasar dai tun a shekarar 1980 lokacin da Christian Chukwu ya jagoranci tawagar kasar ga nasara gaban dubban magoya baya ciki har da shugaban kasar na waccan lokaci Shehu Shagari.

Hadin gwiwar daukar nauyin gasar da Najeriya ta yi tsakaninta da Ghana a shekarar 2000 ya zo da rashin nasara bayan da Kamaru ta lashe kofin yayin wasan karshe da ya gudana a Legas.

A jiya Laraba ce dai aka sanar da wadanda suka yi nasara bayan kammala taron jefa kuri’a da mambobin kwamitin CAF karkashin jagorancin shugaba Patrice Motsepe suka yi a otal din Marriott da ke unguwar Zamalek a cikin birnin Alkahira na Masar.

Patrice Motsepe ya ce, “Babban dalili bai wa Morocco wannan dama shi ne goyon bayan takarar da take na karbar bakuncin Gasar Kofin Duniya ta 2030 tare da Sfaniya da Portugal.”

Morocco ta samu nasara da kuri’u 22, yayin da abokan hamayyarta ciki har da Aljeriya da aka ce ta janye daga takarar a watannin da suka gabata, ba su samu kuri’u ba.

Bayanai sun ce a Yammacin ranar Talata ne shugaban hukumar kwallon kafar Aljeriya ya sanar da janyewar kasarsa daga takarar karbar bakuncin wanda CAF ta ki amincewa.

Wannan shi ne karo na biyu ke nan da Morocco za ta karbi bakuncin AFCON tun bayan wadda ta yi a shekarar 1988 inda ta kare a matsayi na hudu.

Alkaluma sun nuna cewa shawarar da hukumar CAF ta yanke wajen bai wa Morocco wannan dama ba abin mamaki ba ne ganin yadda kasar take zuba jari a fannin wasanni tsawon shekaru 20 da suka gabata.

Kazalika, Morocco na tutiya da manyan filayen wasa na-gani-na-fada da dama, kuma ta yi nasarar karbar bakuncin gasannin kwallon kafa na Afirka da na duniya da dama kuma ta kasance wurin da aka fi so a gasar kwallon kafa a baya-bayan nan inda gasar AFCON ta mata da da ta ’yan kasa da shekara 23,  U-23 AFCON duk ke gudana a kasar.

Ana iya tuna cewa, hukumar CAF ta shiga laluben kasar da za ta karbi bakuncin gasar shekarar 2025, bayan da aka hana wa Guinea mai masaukin baki ‘yancin karbar bakuncin gasar a watan Oktoban da ya gabata.

Rashin wadatattun ababen more rayuwa na filin wasa ya kasance matsala ga galibin kasashen gabashin Afirka, abin da ya tilasta wa kungiyoyin kasashen buga wasannin nahiya a waje.

Gasar ta 2027 za ta zama karon farko da za ta gudana a gabashin Afrika tun bayan shekarar 1976 lokacin da Habasha ta karbi bakuncinta.