Gwamnatin Gombe ta dawo da aikin duba-gari da kuma sharar da ake yi a duk makon karshen wata a Jihar.
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan a yayin halartar aikin share magudanan ruwan a unguwar Dawaki da ke garin Gombe.
Gwamnan na Gombe ya ce gwamnatin jihar za ta kashe Naira miliyan 300 wajen share magudanan ruwa saboda kauce wa aukuwar ambaliyar ruwa.
Za a kuma samar da wuraren zubar da shara guda 180 a Gombe wadanda su ma za su lashe Naira miliyan 83.
Ya ce hakan ya biyo bayan hasashen da aka yi cewa jihohi 27 ciki har da Gombe za su fuskanci matsalar ambaliya a damunar bana.
A cewarsa, sare itatuwa a dazuka ne ke haifar da zaizayar kasa, zuba shara a magudanan ruwa kuma ke sa su cushe har ya kai ga ambaliya.
Gwamna Yahaya, ya gargadi magidanta da su guje wa zubar da shara a magudanan ruwa domin hakan bai dace ba.
A cewarsa, akwai manyan kwarurruka guda biyar da suka dami jihar kuma duka za a duba yiwuwar magance su kamar yadda aka dinke wanda ya tashi daga jami’ar jihar ya bi ta Malam Inna zuwa Kagarawal.
A nata jawabi, Kwamishinar Muhalli da kula da Gandun Daji, Hussaina Danjuma Goje, cewa ta yi kwalbatin unguwar Dawaki shi ne na 13 cikin manyan magudanan ruwa da za a share jihar.
Hussaina Goje, ta ce tsawon magudanan ruwan da za a share ya kai kilomita 23, kuma ma’aikatarta da hadin guiwar hukumar NEWMAP da NASREA ne suka hadu don gudanar da aikin.