✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure shi a kurkuku kan zambar kudin jabu

Bayan ya yi sayayya ya biya, yana tafiya kudin suka koma ganyen zogale

Kotun Musulunci da ke zamanta a unguwar PRP a Kano ta daure wani magidanci mai suna Nuraddin Muhammad Zariya a gidan gyaran hali bisa samun sa da laifin cuta da zamba.

Mai gabatar da kara, Aliyu Abidin, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya je shagon wani Abubakar Musa Danzaki ya sayi katunnan waya na Naira dubu saba’in yana tafiya bai yi nisa ba sai kudin suka koma ganyan zogale.

Nan take aka yi tara-tara aka kama shi aka kuma miqa shi wajen ’yan sanda.

Bayan karanto masa kunshin tuhumar, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda mai gabatar da lara ya roki kotun ta yi masa hukunci nan take.

Kotun kuma ta amince ta yanke masa hukuncin kaurin wata shida a gidan yari, babu zabin biyan tara.