Wata kotu da ke zamanta a yankin Karu a Abuja, ta yanke wa wani matashi mai shekara 27, Halidu Nuhu, hukuncin daurin shekara hudu a gidan yari, bisa samunsa da laifin satar kayayyaki da amfani da tabar wiwi.
Alkalin kotun, Umar Mayana ya yankewa Nuhu hukuncin ne bayan ya amsa laifukan da suka hada da hada baki, barna, sata, cin zarafi da kuma cutar da jama’a, amma ya roki a yi masa sassauci.
- Kotun Birtaniya ta sami Ike Ekweramadu da laifin safarar sassan jikin dan Adam
- APC ta yi barazanar dakatar da Danjuma Goje a Gombe
Alkalin kotun ya bai wa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar N250,000.
Tun da farko, mai gabatar da kara, Edwin Ochayi, ya shaida wa kotun cewa wani mai suna Halilu Abdulrasheed na yankin Kuruduma a Asokoro a Abuja, ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na yankin.
Ochayi, ya ce a ranar 1 ga watan Fabrairu, Nuhu ya hada baki da wani mutum, inda suka shiga wani otal, suka lalata wata mota, sannan ya saci babbar waya.
A cewar Ochayi, a yayin binciken ‘yan sanda, Nuhu da wanda ke taimaka masa sun amsa laifukan yayin da ‘yan sanda suka samu wata wuka da tabar wiwi.
Ochayi ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 327, 397 da 188 na kundin laifuffuka.