Wata Kotun Majistare dake Shagamu a jihar Ogun ta daure wani yaro dan shekara 18 saboda zargin garkuwa tare da kashe wata mata mai suna Alhaja Barakatu Bello.
Ana dai tuhumar matashin a gaban kotun da aikata laifuka uku da suka hada da kisan kai da garkuwa da mutane da kuma hadin baki.
- Mun kama soja dumu-dumu yana ba ’yan ta’adda kaki da albarusai – Gwamnatin Zamfara
- Kotu ta amince da bukatar raba aure bayan miji ya yi wa matarsa kishiya
- Kotu ta ki amincewa da bukatar kwace kadarorin Saraki
Dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Adekunle Opayemi, ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne ranar 4 ga watan Maris na Shekarar 2020 da misalin karfe 10:00 na safe a layin Ajao da ke Aiyepe a garin na Shagamu.
Opayemi ya ce yaron, tare da wasu gungun masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa tare da kashe wata mata ta hanyar harbi da bindiga.
Dan sandan ya kuma ce bayan yin garkuwa da kashe matar, wanda ake zargin ya kuma bukaci kudin fansa inda suka ci gaba da tattaunawa da mijinta har bayan sun kasheta kuma sannan sun wurgar da gawarta gefen hanya.
Dan sandan ya ce sun yi nasarar cafke wanda ake tuhumar ta hanyar amfani da na’urar binciken kwakwaf kan wayarsa ta salula.
Laifin dai a cewar dan sandan ya saba da tanade-tanaden sassa na 324, 23(2) da 24(2) da kuma na 319 na kundin Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Ogun na shekarar 2006.
Alkalin kotun, Miai Shari’a M.O. Oshibajo, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare yaron a gidan kurkukun Shagamu.
Daga nan ne kuma ta dage sauraren shari’ar har zuwa ranar 20 ga watan Maris na shekarar 2021.