✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure matar aure saboda zargin makwabciyarta da maita

An nadi muryar matar a yayin da take cewa makwabciyarta mayya ce.

Wata kotu da ke zamanta a yankin Gwagwalada na babban birnin tarayya Abuja, ta daure wata matar aure mai suna Adama Bello saboda zargin makwabciyarta da maita.

Rahotanni sun ce ’yan sanda sun cafke matar mai shekaru 20 saboda cewa makwabciyarta mayya.

Yayin gabatar da ita a gaban kotu, ’yan sanda sun zargi Adama da bata wa makwabciyartata suna.

Adama ta zargi Zainab Samaila da yunkurin kasheta kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

Bayanai sun ce an nadi muryar Adama yayin da take cewa makwabciyarta mayya ce wanda kuma aka gabatar da rikodin din a gaban kuliya.

Alkalin kotun, Sani Umar ya bayar da belin Adama akan kudi naira 200,000 da kuma mutum daya da zai tsaya mata.

Sai dai ya ce idan ta gaza cika wadannan sharudda a kaita ajiya gidan Dan Kande.