Kotu ta daure wata matar aure ’yar shekara 28 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba, kan laifin zuwa wa kishiyarta ruwan zafi da gangan a lokacin da kishiyar take tsaka da barci.
Babbar Kotun Majistare da ke Gwagwalada a Abuja ta yanke wa matar da ke zaune a kauyen Gosa Toge hukuncin ne bayan an gurfanar da ita kan zargin aikata laifukan cin zarafi da kuma cutar da dan Adam.
Babban alkalin Kotun, N.A Turkur, da ya yanke mata hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni takwas ba tare da zabin biyan tara ba, ya gargade ta da ta daina aikata irin wannan aika-aikar, kuma ta kasance mai kyawawan halaye.
- Rashin tsaro: Za a sauya wa makarantu 359 wurin zama a Kaduna
- Majalisa ta soke harajin tura kudi ta intanet
Tun da farko dai, lauya mai shigar da kara, Dabo Yakubu, ya shaida wa kotun cewa ana tuhumar matar ne da laifin zuba wa kishiyarta ruwan zafi da gangan a lokacin da take barci.
Ya ce, “wadda ake tuhuma ta amsa laifinta tun a gaban ’yan sanda. Ta ce da gangan ta zuba wa kishiyarta ruwan zafi”.
Yakubu ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 267 da sashe 268 da kuma na 247 na kundin laifuffuka.
(NAN).