Runduar ’yan sandan IRT mai aikin ko-ta-kwanta ta cafke wasu mata hudu da ke kai wa ’yan bindiga karuwa da miyagun kwayoyi a cikin daji a Jihar Kaduna.
Mai magana da yawun hukumar ’yan sandana Najeriya, Frank Mba, ya ce matan ta cika ne bayan an gano yadda suke hada baki da ’yan bindiga har suke musu safarar karuwai don sheke ayarsu.
- An cafke ’yar aikin da ta kashe mahaifiyar tsohon Gwamnan Edo
- Mawaki Umar M. Shareef ya zama jakadan gidan talabijin na Qausain
Mba ya kara da cewa matan da suka shigaba hannu na kuma kai wa wani dan bindiga mai suna Isah Ibrahim bayanan sirri.
Ya bayyan cewa an same su da muggan makamai da kwayoyi a yayin samamen da rundunar IRT ta kai a maboyarsu.
Matan dai na cikin wasu mutum 26 da aka kama kan zargin aikata laifuka daban-daban, wadanda aka gabatar da su a Hedkiwatar Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da ke Abuja.
Kakakin ’yan sandan ya shaida wa manema labarai cewa, za a mika su zuwa ga kotu bayan kammala bincike don a yanke musu hukuncin da ya dace da su.