Bisa dukkan alamu an dage zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka saba gudanarwa a duk ranar Laraba.
Zuwa karfe tara 9 na safiya (lokacin da aka saba fara zaman) a wannan Larabar, dakin taron ya kasance a rufe.
- ’Yan bindiga sun kai hari NDA, sun kashe soja, sun sace hafsoshi
- Majalisar Zamfara ta daina zama bayan garkuwa da mahaifin shugabanta
Sannan ba a ga isowar ministoci da sauran mambobin Majalisar Zartarwar da suka saba halartar zaman ba a Fadar Shugaban Kasa.
Kazalika babu wata sanarwa daga fadar gwamnatin da ta bayyana dalilin rashin yin zaman, ko da yake a makon da ya gabata an gudanar da irinsa.
Masu hasashe na zargin hakan ba zai rasa nasaba ba da abin da ya faru ranar Laraba na harin da aka kai wa Makarantar Horas da Kananan Hafsoshin Sojin Najeriya (NDA) da ke Kaduna.
A harin na daren Talata zuwa wayewar gari, ’yan bindigar da suka kutsa har rukunin gidajen hafoshin da ke cikin barikin sun kashe hafshohin soji biyu suka kuma yi garkuwa da wasu biyu, sannan suka bar wani wani da raunin harbi.
Lamarin dai ya zo wa mutane da ban mamaki, inda ’yan Najeriya ke bayyana shi a matsayin babban abin kunya da ke nuna tsananin raunin tsaro a Najeriya.