Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dage sauraron shari’ar da wani matashin mawaki, Abdul Kamal, ya maka BBC Hausa kan amfani da sautin wakarsa a matsayin taken shirin ‘Daga Bakin Mai Ita’ ba tare da izininsa ba.
A yayin zaman kotun na ranar Litinin, Sashen Hausa na BBC ya nemi kotun ta yi watsi da bukatar mawakin mai suna Abdul Kamal, na biyan s wasu kudi a matsayin diyya daga kamfanin.
- Gidan Malam Aminu Kano da abubuwan da ke ciki
- NAJERIYA A YAU: Mece Ce Makomar Jam’iyyar APC A Jihar Kano?
Lauyan BBC, Barista Shakiruddedn Mosobalage, ya bayyana cewa tun da masu kara sun bayyana kudin da suke nema a matsayin tarar amfani da abin da suke kara, to babu bukatar kotu ta bayar da wata oda a kan hakan.
Abdul Kamal ya maka BBC Hausa a gaban kotun ne kan yin amfani da wani sautin kidansa a matsayin taken shahararen shirinsu na ‘Daga Bakin Mai ita’ ba tare da izininsa ba.
Lauyansa, Barista Bashir Ibrahim Umar, ya bayyana cewa rokonsu na kan daidai kuma kotu ba ta hurumin yanke wa mutum abin da zai nema a matsayin diyya.
“Idan mai kara ya kai kara dole ne zai fada wa kotu abin da yake so ta yi masa, ba wai ita kotun ce za ta ce ga abin da za a yi wa mai kara ba.”
Alkalin kotun, Mai Shari’a N.M Yunusa, ya dage zaman zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu, 2024 don ci gaba da shari’ar.